Tuesday, 23 October 2018

Takarar shugaban kasa: Omoyele Sowore ya zabo mataimakinsa daga jahar Jigawa

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar AAC, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters ya zabo mutumin da zai tsaya masa takarar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar 2019, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.


Daraktan yakin neman zaben Sowore, Malcol Fabiyi ne ya sanar da haka a ranar Litinin, inda yace a iya bincikensu, basu ga wani mutumin da ya cancanta ba kamar Dakta Rufai Ahmad.

Shima a nasa jawabin, mai gaya mai aiki, Omoyele Sowore ya tabbatar da cancantar Ahmad Rufai, musamman yadda yake kwararren likita wanda zai iya kawo sauyi mai ma’ana a harkar kiwon lafiya a gwamnatinsu idan ya kai labari.

“Lafiya jari ne, kuma gwamnatinmu za ta tabbatar da ganin duk dan Najeriya ya samu kiwon lafiya mai inganci wanda zai taimaka wajen cigaban tattalin arzikin kasa, don haka ban yi zaben tumun dare ba, don kuwa Ahmad Rufai daidai yake da gabatar da aikace aikacen nan.

“A kokarinmu na kawo gyara ga dimbin matsalolin Najeriya don daukaka martabar kasa, muna da yakinin cewa kiwo lafiya na daga cikin muhimman fannonin da zamu basu kulawa, saboda haka ban jin akwai wanda zai iya kawo gyaran nan kamar Dakta Rufai.” Inji shi.

A shekarar 1979 aka haifi Rufai a jahar Jigawa, inda ya yi karatun digirin Likitanci, MBBS, a jami’ar Bayero ta Kano, sa’annan yayi karatun digiri na biyu a jami’ar Leeds dake Birtaniya, yana da rajista da kwalejin likitocin Afirka ta kudu.

Ahmad Rufai ne shugaban tsangayar ilimin kiwon lafiya na farko a jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Dutsen jahar Jigawa, haka zalika ya taba zama kwararren likita a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake Birnin Kudun jahar Jigawa.

Daga cikin fannonin kiwon lafiya da Rufai ya kware akwai kiwon lafiyan mata da kananan yara, cututtuka masu yaduwa, tsare tsare ciyar da kiwon lafiya a matakin farko gaba, tsare tsaren inganta kiwon lafiya, da dai sauransu.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment