Friday, 12 October 2018

Taron dangin 'yan siyasa ba zai hana Buhari cin zabe ba>>fadar shugaban kasa

Bayan sasantawar Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, Fadar shugaban kasa ta hannun masu magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu da kuma Femi Adesina hadi da kungiyar yiwa shugaban kamfe duk sun mayar da martani akan wannan hadaka ta Atiku da Obasanjo.


Obasanjo dai yace ya yafewa Atikun laifin da yayi mishi a baya kuma yana goyon bayanshi ya zama shugaban kasar Najeriya a PDP, Atikun ya samu rakiyar manyan malman addinin kirista dana Muslunci.

Fadar shugaban kasa ta hannun Femi Adesina tace, babu wani taron dangi da wasu 'yan siyasa zasu yi da zai sa shugaba Buhari ya fadi zaben shekarar 2019. Yace karfin hadakarsu ba zai hana su faduwa ba.

Shima Garba Shehu yace, fadar shugaban kasa ta samu labarin hadewar ta Atiku da Obasanjo kuma basu yi mamaki ba amma abinda suka sani shine wannan ba zai janye hankalin shugaba Buhari daga ayyukan dake gabanshi ba na raya kasa da samar da tsaro ba.

Yace da Atikun da wanda suka hada kai tare zasu fadi.

Itama kungiyar yakin neman zaben Buharin tace lallai tsinuwar da Obasanjo ya jawowa kanshi da kanshi zata kamashi kuma 'yan Najeriya ba zasu bishi ba, domin da kanshi a 'yan kwanakin baya yace idan ya goyi bayan Atiku Allah ma bazai yafe mishi ba amma gashi yau shine yace ya yafe mishi.

Kungiyar ta kuma soki malaman addinai da suka jagoranci sasanta Atiku da Obasanjon inda tace ta kara bayyana a fili ga 'yan Najeriya irin sukar da sukewa Buhari a baya ashe ga aniyarsu.

Ta karkare da cewa 'yan Najeriya ba zasu yadda a dawo musu da gwamnatin rashawa da cin hanci ba.

No comments:

Post a Comment