Friday, 5 October 2018

Tsohon dan wasan Man U ya roki kungiyar kada ta kori Mourinho

Mai horar da tawagar kwallon yankin Wales na Birtaniya, kuma tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs, ya shawarci kungiyar da ta kara hakuri da mai horar da 'yan wasanta Jose Mourinho kada ta kore shi.


Giggs ya ce koda yake United na fuskantar kalubale a halin yanzu, yana da kwarin gwiwar lamarin zai sauya, kuma nasara zata sake ziyartar kungiyar.

Mourinho na fuskantar suka daga ciki da wajen kungiyar ta United, ganin yadda ya jagoranci wasanni hudu ba tare da samun nasara ba, a gefe guda kuma, ga rashin kyakkyawar alakar dake dada bayyana tsakaninsa da Paul Pogba, dan wasan kungiyar mafi tsada.

A baya bayan nan dai wasu daga cikin masu sharhi kan wasanni, na da ra'ayin zai yi wahala a ce kungiyar ta United bata sallami Mourinho, ida wasu ke zaton cewa mai yiwuwa tsohon mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya maye gurbinsa.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment