Monday, 1 October 2018

Tsohon shugaban EFCC Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamnan APC a Adamawa ya kafa hujja

Tsohon shugaban EFCC, Mallam Nuhu Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamna dake gudana a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Adamawa.


Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an tantance Ribadu, Mahmood Halilu da gwamna Muhammadu Bindow mai ci a yanzu don su kara a zaben fidda gwani na ranar Lahadi.

Wata sanarwa daga darakta janar na kungiyar yakin neman zaben Ribadu, Mallam Salihhu Bawuro, yace Ribadu ya yanje ne bisa ga tsarin zaben fidda gwanin.

“Yayinda mu da mafi akasarin yan APC a jihar Adamawa suka goyi bayan bayar da mulki ga mutane ta hanyar zaben fidda gwani na kato-bayan-kato, jam’iyyar ta yanke shawarar yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai a karshe.

“Mu duka mun zata za’a mutunta burin mambobin jam’iyyar mafi rinjaye, sannan ayi aiki dashi. Amma shawarar da aka yanke na yin akasin haka yasa mu da magoya bayanmun muka janye.

“Muna adawa da amfani da zaben fidda gwani na wakilai ne saboda muna ganin an saba ka’idar tsarin da muke sa ran zai kawo kowa ya gwada sa’arsa

“Don haka bama ganin adalci a hannun wadanda ake kira da jami’an jam’iyya."

Ya kuma jadadda jajircewar Ribadu na ci gaba da kasancewa a APC da kuma ci gaba da marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.
Naija.ng.


No comments:

Post a Comment