Friday, 5 October 2018

Tsohon yaron Jonathan ya lashe zabe a APC

Labari ya zo mana daga Jaridun kasar nan cewa tsohon Hadimin Shugaba Goodluck Jonathan zai yi takarar kujerar ‘Dan Majalisar Tarayya a Jihar Imo a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a 2019.


Yanzu haka Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsaida Ima Niboro a matsayin wanda zai rike mata tuta a zaben Yankin Udu da Ughelli a Majalisar Tarayyar Imo. Niboro ya bar PDP ya koma Jam’iyyar APC ne a karshen 2016.

Niboro ya taba aiki a matsayin mai taimakawa Jonathan lokacin yana fadar Shugaban kasa. Daga baya kuma tsohon Shugaban kasar ya nada Niboro a matsayin Shugaban Hukumar dillacin manema labarai na kasa watau NAN.

Chris Onojiacha shi ne Malamin zaben fitar da gwanin na APC wanda ya sanar da cewa Imo Niboro ya samu kuri’a 438. Mista Niboro babban ‘Dan Jarida ne wanda ya canji Remi Oyo a NAN bayan wa’adin ta ya cika a 2013.

‘Dan takarar ya doke mutane 4 a zaben wanda su ka hada da Rukevwe Ugwumba; Francis Ejiroghene Waive; Andrew Orugbo da kuma wani Akpovoka Efeni. Niboro yana sa rai a zabe sa a babban zaben da za ayi a badi 2019.

Jiya kun ji cewa wani Hadiman Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu tikitin takarar kujerar Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar APC na Yankin Tarauni a Jihar Kano.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment