Thursday, 18 October 2018

Twitter ya yi wa Rasha da Iran tonon silili


Kamfanin Twitter ya fitar da dukkan sakwanni miliyan goma da masu alaka da Rasha da Iran ke wallafawa, don kokarin sanyawa mutane ra'ayi a siyasar kasashen duniya.Wasu daga sakwannin an wallafa su ne tun a shekarar 2009, lokacin da ya wuce wanda ake hasashe na zaben shugaba Trump na Amurka da aka yi na baya-bayan nan da ake zar
gin Rasha da hannu a ciki.

Sakwanni dubu hudu da aka wallafa dai hukumomin kasar Rasha daban-daban ne suka wallafa, da ake kyautata zaton suna da hannu a gangamin yada bayanan da ba su da tushe bare makama a shafin internet.

Masu sharhi sun ce yawanci mutanen sun yi badda kama a matsayin Amurkawa, da kuma suke wallafa kalamai da bayanan bogi kan 'yar takarar shugaban kasa Hillary Clinton.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment