Friday, 26 October 2018

UEFA zata hukunta Man United bisa abinda suka wa Ronaldo

A wasan da aka buga na gasar cin kofin zakarun turai na farkon makonnan, ranar Talatar da ta gabata, tsakanin kungiyoyin Manchester United da Juventus a filin wasan Man U din, an samu wasu 'yan kallo sun yi kutse dan haduwa da Ronaldo wanda tsohon dan wasan kungiyarne.Ana tsaka da wasa, an samu wani ya shigo inda ya tunkari Ronaldo, amma jami'an tsaro sun rikeshi kamin ya karasa gareshi duk da Ronaldon ya gaisa dashi.

Haka kuma bayan kammala wasan, wanda ya kare Juve na cin Man U 1-0, an sake samun wasu mutum 2 sun yi kutse cikin filin wanda suma duk suka nufi Ronaldon.

Wannan dalili yasa hukumar kula da wasannin turai ta UEFA ta tuhumi kungiyar Man United akan rashin da'ar 'yan kallonta. Skysport ta ruwaito cewa za'a yi zama ranar 22 ga watan gobe dan tattauna hukunci da kuma tarar da kungiyar zata biya akan wannan abu da ya faru.

Ronaldo dai ya dauki hoton Selfie da daya daga cikin 'yan kallon da yayi kutse duk da cewa jami'an tsaro na rike dashi, kuma jami'an 'yansanda sun tabbatar da cewa akwai wani mutun dan kimanin shekaru 40 da ake tsare dashi bisa laifin kutse a cikin filin wasan

No comments:

Post a Comment