Saturday, 6 October 2018

Wakilan APC sun mutu jim kadan bayan kada kuri'ar su a zaben fidda gwani

Jam'iyyar APC ta rasa wasu wakilai masu jefa kuri'a a zaben fitar da gwani daga mazabar Arewa-maso-Gabas a jihar Jigawa. Wakilan sun mutu ne awanni kadan da jefa kuri'arsu a zaben fitar da gwani na kujerar Sanatan mazabar Jigawa ta Arewa-maso-Gabas.

Mummunan hatsarin mota ne ya zama silar mutuwar wakilan, bayan da suka je karamar hukumar Gumel don jefa kuri'arsu, a hanyarsu ta komawa karamar hukumarsu, Guaiwa, bayan jefa kuri'asu da misalin karfe goma da rabi na yammacin Juma'a.

Da ya ke tabbar da faruwar wannan mummunar hatsarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Jigawa, SP Abdul Jinjiri, ya ce, "hadarin ya auku a wani kauye da ke kan hanyar Gumel zuwa Babura mai suna Dantado. Hatsarin ya rutsa da karamar mota kirar Gulf 3 tare da wata mota kirar bas mai lamba, DB 421 KZR."

SP Jinjir ya labarta yadda hatsarin ya auku da cewar, "Su duka motocin na dauke da wakilan jam'iyyar APC da suka jefa kuri'a a karamar hukumar Gumel, suna kan hanyar komawarsu Guaiwa. Kasancewar suna matsanancin gudu, a lokacin da direban bas din ya yi kokarin wuce karamar motar, sai suka gogi juna, hakan ya sa motar ta kwacewa direban.

"Motar na kwacewa sai suka afka daji, wannan yasa motar bas din jujjuyawa tana wulkitawa har dai ta kashe mutanen da ke ciki gaba dayansu har da matukin motar, a nan take."

Da ya ke mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu dama jihar Jigawa, gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, ya ce ya kadu matuka da jin labarin mutuwarsu.

Ya ce, mamatan sun ketare duk wahalhalu suka zo Gumel domin cin moriyan ‘yancin su, su kuma sauke nauyin da ke hansu a matsayin su na wakilai, domin su zabi shugabannin da za su jagoranci kasa.
Naija.ng

No comments:

Post a Comment