Monday, 8 October 2018

Wani gwamna ya bayyana babban dalilin da yasa Atiku ya lashe zaben fidda gwani na PDP

Bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na PDP, Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku ya bayyana babban dalilin da yasa Atikun ya lashe zaben.

Gwamnan ta hannun me magana da yawunshi, Bala Dan Abu ya bayyana cewa, so da kuma  jajircewar Atiku wajan ganin ya bautawa kasarshine yasa ya kai ga nasarar lashe zaben fidda gwanin na PDP.

Ya kuma yaba da yanda aka gudanar da zaben cikin tsari da nuna kishin kasa hakanan ya yabawa sauran 'yan takara saboda halin dattakon da suka nuna.

A karshe yace nasara na tare da jam'iyyarsu ta PDP a zabe me zuwa.

No comments:

Post a Comment