Monday, 29 October 2018

Wani gwamnan APC ya kammala shirye-shiryen sauya jam'iyya

Da alamu dai rikicin cikin jam'iyyar dake mulki a Najeriya, ta All Progressives Congress (APC) zai dauki wani sabon salo biyo bayan labaran da muke samu na kammala shirye-shiren ficewa daga jam'iyyar da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun yayi.

Binciken da majiyar mu ta jaridar Punch tayi dai ya bayyana cewa gwamnan yana sunsunar jam'iyyar adawa ta Democratic Peoples Party (DPP) ne kuma tuni har ma wasu makusantan sa da abokan siyasar sa sun soma shiga jam'iyyar.

Wannan dai ya biyo bayan rashin adalcin da gwamnan yace jam'iyyar ta sa tayi masa tare da magoya bayan sa a lokacin zabukan fitar da gwanin da ta shirya a jihar.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment