Saturday, 13 October 2018

Wani matashi ya fara tafiya a Keke daga jiharshi zuwa Abuja dan ya ga Atiku

Wani mutum daga jihar Imo me suna, Evangelist Uche Debem ya fara tafiya a kan Keke daga jihar tashi zuwa Abuja dan ya hadu da gwaninshi dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da mataimakinshi Peter Obi dan ya taya su murnar lashe zaben fidda gwani.


Mutumin yace yana wannan tafiyane dan ya nuna irin rashin amincewarshi akan irin yanayin da Najeriya take ciki da kuma fatan gwaninshi Atiku zai warware matsalar idan ya zama shugaban kasa.No comments:

Post a Comment