Friday, 26 October 2018

Wani Musulmi ya kusa mutuwa a sanadiyyar rikicin Kaduna amma Kirista ya cece shi

Wannan rayuwa ba matabbata bace, don haka ake fatan kowa yayi amfani da dan lokacin daya rage masa a rayuwa wajen amfanar da abokan zamansa, kamar yadda wani Kirista ya taimaki wani Musulmi ta hanyar cetar rayuwarsa daga mutuwa.

Wani matashin Kirista daga jahar Kaduna mai suna Lord Beckson Sirjoe ya bayyana a shafinsa na Facebook yadda ya ceci wani Musulmi mai sana’ar sayar da dabino da kwakwa, Malam Umar a unguwar Sabon tasha wanda ya kwashe kwanaki 5 ba ci ba sha saboda rikicin Kaduna.


Sirjoe ya bayyana cewa “Na shiga wani gida a titin Black dake Sabon tasha, da na shiga wani daki d babu kowa a ciki sai na tarar da mutum a cikin katakon ajiyan kaya ‘Wardrobe’, yana tsaye kikam, ya gaji ya lalace sakamakon dadewar da yayi a ciki.

“Tun ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba yake cikin wardrobe bayan barkewar rikicin Kaduna, inda ya boye don gudun kada a kasheshi, amma masu gidan basu san yana ciki ba, har sai da na tsinceshi a ciki. Anan na dauke shi tunda ba zai iya tafiya ba.

“Bayan ya dawo cikin hayyacinsa, sai na kira wani mutum Alhaji Hassan don ya tabbatar mana daya sanshi kafin ya mika shi ga hannun jami’an Yansanda.” Inji Sirjoe.
Daga karshe Sirjoe ya bayyana bukatar samun dawwamammen zaman lafiya a Najeriya, amma fa sai mun kasance masu yadda da juna ba tare da lura da bambance bambancen addini da na kabilanci dake tsakaninmu ba.

A ranar Alhamis, 18 ga watan Oktoba ne aka fara samun yamutsi a garin kasuwar Magani a tsakanin Musulmai da Kirista, sai kuma a ranar Lahadi aka dauka a garin Kaduna, wanda yasa gwamnatin jahar ta kaddamar da dokar hana shiga da fita a jahar wanda har yanzu ake cikinsa.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment