Wednesday, 24 October 2018

Wani ya dane kan karfen talla yace bazai sauko ba sai Buhari ya sauka daga mulki

A yaune jama'ar jihar Adamawa suka ga wani abin mamaki da ya faru a kusa da kasuwar Jimeta inda wani mutum me matsakaicin shekaru da ake kira da suna, Lawal Faro ya hau zungureren karfen talla, kamar yanda ake gani a wannan hoton yace ba zai sauko ba sai Buhari ya sauka daga mulki.Lawal ya bayyana cewa, talauci da yunwa da rashin adalci sun yi yawa tsakanin mutane dan haka dole Buhari ya sauka ya baiwa wani, misalin Atiku dan ya canja wannan hali da kasar take ciki.

Lawal dai yace bazai sauko daga kan wannan karfe ba sai Atiku ko kuma wani makamancinshi yazo ya tabbatarmai da cewa za'a kawar da mulkin APC a zaben 2019, sannan yayi alkawarin kwashe awanni 12 akan wannan karfe kamin ya sauko.

Saidai rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da yake kan wannan karfe a makale, mutanen da suka taru a kasa suna kallon ikon Allah sun rika shewar 'Sai Buhari".

No comments:

Post a Comment