Friday, 5 October 2018

Wannan handama har ina?: Karanta yawan kudin da Afrika ke asara duk shekara saboda sata

Kungiyar Kasashen Afrika ta ce, nahiyar na asarar Dala biliyan 80 kowacce shekara sakamakon halarta kudaden haramun ta hanyar fita da dukiyar yankin zuwa kasashen duniya ta hanyar da ba ta kamata ba.


Yayin gabatar da wani rahoto kan yadda ake halarta kudaden haramun a wani taro da kungiyar kasashen Afirka ta shirya, tsohon shugaban Afrika ta kudu, Thabo Mbeki ya ce adadin kudaden da ake safarar su ya karu daga Dala biliyan 50 a shekarar 2015 zuwa Dala biliyan 80 kowacce shekara.

Mbeki da ke jagorancin kwamitin da ke yaki da halarta kudaden na haramun a kasashin kungiyar kasashen Afrika ya bayyana damuwa kan irin asarar da Afrika take tafkawa, wanda ya ce yana matukar tasiri kan gwamnatocin nahiyar wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu.

A nashi jawabi, shugaban hukumar tara kudaden haraji ta Najeriya, Tunder Fowler ya ce kashi 40 na wadannan kudade da ake safarar su, na fitowa ne daga Najeriya.

Jami’in ya bayyana hanyoyi guda 3 da ake amfani da su da suka hada da manyan kamfanonin kasashen waje da cinikin man fetur da iskar gas da kuma hada-hadar bankuna.
Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya ce, kasar na daukar matakan rage cin hanci da rashawa da kuma halarta kudaden haramun da ake samu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment