Friday, 19 October 2018

Wasan Chelsea da Man Utd: Jose Mourinho na tsaka mai wuya

A ranar Asabar ne Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a Stamford Bridge, a wasan mako na tara na Premier, wanda ke da matukar muhimmanci ga kociyan United din Jose Mourinho ganin irin tsaka-mai-wuyar da yake ciki kan matsayin kungiyar a tebur, inda yanzu take ta takwas da maki 13 a wasa takwas.


Shekara biyu da ta wuce a wannan makon Mourinho wanda ke cikin matsi ya jagoranci kungiyar tasa ta je gidan Chelsea wadda ta casa ta.

A lokacin united tana da maki 14 a wasanninta takwas na farko na gasar, kuma tana matsayi na bakwai a teburin Premier.

Mourinho wanda kungiyar ta dauko da fatan shi ne zai fitar da ita daga halin da take ciki na koma-baya, sai ya kasance bai ba wa marada kunya ba, babu wani sauyi na sosai da ya kawo mata.

A wannan wasa na ranar cikin dakika 30 kacal da take leda Chelsea ta daga ragar bakin nata, kuma zuwa karshen karawar ta casa United da ci 4-0.

Wannan rashin nasara ya zamar wa Mourinho tsohon kociyan Chelsean wanda magoya bayan kungiyar suka rika tsokana, mafi muni a dukkanin wasannin da ya jagoranta tun watan Nuwamba na 2010.

Kuma sakamakon ya kasance mafi muni da United ta gani a gasar Premier a wasan waje tun shekara ta 1999.

To a wannan kakar kuma Red Devils din sun gaza da maki daya a wasanninsu takwas na farko kuma sun yi kasa da mataki daya a teburin gasar ta Premier idan aka kwatanta da wancan lokacin.

Bugu da kari har yanzu ba su hadu da Manchester City da Liverpool ba sabanin a kakar 2016/17 da suka riga suka fafata zuwa yanzu.

To yanzu ga shi za su sake zuwa Stamford Bridge. Idan har Chelsea ta sake maimaita musu abin da ta yi musu a wancan lokacin ta lallasa su, to hakan ba shakka zai kai Mourinho ya baro shi.

A halin yanzu Manchester United tana fuskantar wasa shida wadanda kila su sa ta san matsayinta a bana da kuma makomar kociyanta Mourinho.

Bayan wasanta na ranar Asabar a gidan Chelsea, United din za ta karbi bakuncin Juventus a gasar Zakarun Turai, sannan ta kara karawa a gida da Everton, kafin kuma ta tafi gidan Bournemouth, daga nan ta je ramako Turin gidan Juventus sannan ta kammala da wasan hamayya na Manchester a filin City.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment