Wednesday, 3 October 2018

'Wasu iyayen basu tada 'ya'yansu zuwa sallar Asuba saidai su tashe su zuwa makaranta'

Wata baiwar Allah me amfani da shafin Twitter ta koka akan yanda yanzu wasu iyaye basa tada yara zuwa sallar Asuba, saidai idan gari ya waye a tashe su zuwa makaranta.


Tace, yanzu Allah ya kawo mu wani zamani da saidai a tashi yara zuwa makaranta amma ba za'a tashe su zuwa sallar Asuba ba. Domin ci gaban Al-ummar mu ya kamata wannan halayya ta canja.

Jama'a da dama dai sun gamsu da wannan jawabi nata.

No comments:

Post a Comment