Friday, 12 October 2018

Wasu Kiristoci A Jihar Filato Sun Soma Azumin Kwanaki 40 Don Ganin Buhari Ya Ci Zaben 2019

Wasu mabiya addinin Kirista a jihar Filato sun soma azumin kwanaki 40 don ganin shugaba Muhammadu Buhari ya sake samun nasara a zaben 2019.


Kiristocin karkashin kungiyar 'National Inter-Faith and Religious Organisations for Peace (NIFROP)' suna kuma kan yi wa kasa addu'a domin samun zaman lafiya.

A jawabin da ya yi a jiya Laraba, jagoran addu'ar, Bishop Sunday Garuba ya bayyana cewa Allah ne ya aiko Buhari domin ceto Nijeriya daga durkushewa.

Garuba ya kara da cewa makiya Nijeriya za su ji kunya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment