Saturday, 20 October 2018

Wasu Malaman Arewa Ba Sa Son Atiku Amma Allah Yana Tare Da Shi>>Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa akwai wasu malamai dake Arewacin kasarnan da basa son dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Ga abinda Lamidon ya fada kamar haka:

"Na fara Siyasa daga wannan kauyen namu (Bamaina) a lokacin babu wanda ya san ni. A hankali a hankali nake tafiya Allah yana dafa min yana kuma yi mini jagoranci. Na yi takarkaru kala-kala babu adadi, na yi nasara kuma na fadi, na ci zabe ma an murde, amma dai cikin nufin Allah da ikon sa ban taba yin fushi da duk hukuncin da Allah ya yi a kaina ba. 

"Babu wanda ya san yadda aka yi na zama minista da sauran mukaman da suka daga daraja ta har kuka san ni duk daga Allah ne.  

"Obasanjo da sauran manyan Nijeriya har da Malaman Arewa duk ba sa son Atiku amma kuma shi Allah ya bawa. Dan haka mun karba za mu yi shi domin zabin Allah ne", Inji Dr Sule Lamido.
Rariya.

No comments:

Post a Comment