Sunday, 7 October 2018

Wata jami'ar kasar waje ta baiwa Ali Nuhu digirin girmamawa na Dacta

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki ya samu wata gagarumar karramawa daga wata babbar jami'ar kasar Benin me suna ISM Adonai, jami'ar wadda ke da alaka da jami'ar kasar Amurka dake jihar Florida ta baiwa Ali Nuhu digirin Dakta na girmamawa.Ta bayyana kwazo da jajircewar Ali Nuhu wajan aikinshi na fim da gudummuwar da ya bayar ga al'umma a matsayin abinda ta yi la'akari dashi wajan bashi wannan Digiri.

Muna tayashi murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment