Friday, 19 October 2018

Wenger zai koma fagen horar da kwallon kafa

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce, yana saran komawa fagen aikin horarwa nan da ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa bayan neman da kasashen duniya ke yi masa.


A karshen kakar da ta gabata ne Wenger mai shekaru 68 ya kawo karshen zamansa na shekaru 22 a Arsenal.

Sai dai tsohon kocin ya ce, akwai yiwuwar ya koma horar da tawagar wata kasa ko kuma ya koma Japan, in da ya taba horar da Nagoya Grampus Eight.

Wenger ya shaida wa jaridar Bild ta Jamus cewa, yanzu ya huta sosai, kuma a shirye yake ya koma bakin aikin bayar da horo, amma bai bayyana takamammen in da zai koma ba.

A can baya, an yi rade-radin cewa, gwarzon kocin zai koma PSG ta Faransa don aiki tare da Thomas Tuchel.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment