Saturday, 13 October 2018

Ya Saki Matarsa Saboda Wani Ya Sa Hoton Ta A Instagram A Jihar Kebbi

Auren matar ya mutu ne bayan mijinta ya samu wani ya dora hotonta a shafin sadarwa na Instagram. 

Matar da ta nemi na boye sunanta tace wani ne ya yaudareta har ta tura masa hotonta amma daga karshe hakan ya ja aurenta ya mutu. 

Matar ta dauki Alkur'ani ta rantse da shi akan cewa wallahi bata mu'amala da maza duk domin mijin ya yadda da ita amma yace ta tafi gidansu kawai. 

Tayi kokarin ganin mijinta ya fahimceta amma Yaki saurarta, ta nemi a sata a addu'a akan Allah yasa mijinta ya saurareta ya gane cewa bata yi hakan da gan gan ba kaddara ce kawai ta zo mata.

Matar cikin yanayi na damuwa ta Kasa bayyana yadda akai har ta turawa wani hotonta, amma tace idan har mijinta zai saurareta zata fada masa ko ya akai hakan ta kasance.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment