Friday, 12 October 2018

Ya Shiga Halwa Na Kwanakin 90 Don Ganin Atiku Ya Yi Nasara A Zaben 2019

Wani Bawan Allah da ake kira da Dasukin Baba Atiku ya shiga halwa na tsawon kwanaki 90 don ganin Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben shugaban kasa na 2019. Inda ya ce ba zai fito ba har sai an rantsar da Atiku a matsayin shugaban kasa.Mutumin, wanda yake da zama a unguwar Farawa dake kan titin Maiduguri a karamar hukumar Nasarawa cikin birnin jihar Kano, kafin ya shiga halwar, ya kara da cewa za a dinga sauke kur'ani kullum a gidansa duk don ganin Atiku ya yi nasara.

Kafin shiga halwar da Dasuki zai yi, sai da ya shiga wata halwar ta tsawon kwaniki talatin don ganin Atiku ya ci zaben fidda gwani da aka gudanar, inda kullum sai an sauke Kur'ani a gidansa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment