Wednesday, 31 October 2018

'Yan kabilar Ibo sun sanar da wanda za su zaba a matsayin shugaban kasar Najeriya

Mataimakin wata kungiyar kiristoci a Najeriya kuma mamba a majalisar koli ta masarautun gargajiyar 'yan kabilar Ibo Eze Dakta Oliver Ohanwe ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya kwantar da hankalin sa game da 'yankin Inyamurai domin kuwa shi za su zaba.

Eze Ohanwe da ke zaman Sarkin masarautar Ihim dake a karamar hukumar Isiala Mbano a cikin jihar Imo ya bayyana cewa su sun riga sun gama yin lissafin su sun gano zabar shugaba Muhammadu Buhari ne kawai zai basu damar samun dan kabilar su ya zama shugaban kasa a 2023.

Ohanwe ya bayyana cewa duba da kyawawan manufofin shugaba Buhari da kuma son mulki ya dawo masu a 2023, babu makawa sai sun zabi jam'iyyar ta APC.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment