Sunday, 28 October 2018

'Yan luwadi da madigon Najeriya sun bayyana wanda zasu zaba a 2019

Kungiyoyin 'yan luwadi, madigo da kuma 'yan daudu a Najeriya watau L8sbian, Gay, Bi3exual, and Transgender (LGBT) a turance sun bayyana matukar jin dadin su da jam'iyyar PDP ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su na shugaban kasa a 2019.

Kungiyoyin dai sun kara da cewa su daman tuni sun yake hukuncin mara ma sa baya domin a cewar su, ba zai tauye masu 'yancin su ba na rayuwa kuma shi daman can baya da ra'ayin rikau irin na Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Shugaban gamayyar kungiyoyin a yankin yammacin Afrika Msita Spinky Victor Lee ya bayyana hakan inda yace bayan sun yi duba na tsanaki akan dukkan 'yan takarar, sun yake hukuncin marawa Atiku baya.

A wani labarin kuma, Hukumar Hizbah dake da alhakin tabbatar da da'a a tsakanin al'umma ta jihar Kano dake a Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke wani kasurgumin kwarto da ya shahara wajen yin lalata da matan aure.

Daya daga cikin kwamandojin Hizbah din kuma mai magana da yawun ta, Ustaz Salisu rijiyar Lemo shine ya sanar wa da al'umma hakan a cikin wani dogon rubutu da yayi a shafin hukumar na dandalin sadarwar zamani.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment