Thursday, 25 October 2018

'Yan sanda sun cafke mutumin da ya hau dogon karfe saboda tsanar mulkin Buhari

Labarin da muke samu na nuni ne da cewa wannan mutumin mai suna Lawal Faro da aka kiyasta shekarun sa da kusan 40 da kuma akace ya haye dogon karfe har sai Shugaba Buhari ya dawo yanzu haka yana hannun 'yan sanda.


Kamar dai yadda muka samu, Lawal Faro yanzu haka yana a ofishin 'yan sanda na garin Jimetan Yola inda yake ansa tambayoyi game da abun da yayi.

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake karin haske game da yadda lamarin ya auku, Lawal Faro ya ce wasu 'yan sanda suka yaudare shi suka ce ya sauko za su kai shi wajen Atiku amma yana saukowa sai kawai suka kama shi.

Ya kara da cewa shi har yanzu bai daddara ba, da zarar sun sake shi zai koma saman karfen kuma kamar yadda yayi alkawari, sai dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya tabbatar masa da cewa zai hambarar da gwamnatin Buhari sannan zai sauko.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment