Thursday, 4 October 2018

'Yan wasan Najeriya na neman karo-karon kudi

Yayin da ya rage sauran makonni uku a fara Gasar Cin Kofin Duniya ta Nakasassu a kasar Mexico, tawagar 'yan wasan Najeriya sun fara neman al'umma su tara musu kudi ta hanyar karo-karo don halartar gasar.


Tawagar mai suna Special Eagles ba su samu damar zuwa gasar ba karo uku a baya wato a shekarar 2010 da 2012 da kuma 2014 saboda rashin kudi.

Dan wasan kungiyar nakasassu ta Arsenal Michael Ishiguzo ya fahimci halin da suke ciki, kuma dan wasan wanda yake zaune a birnin Landan ya kafa asusun neman taikama wa 'yan wasan da sunan GoFundMe, inda ake neman tara dala 68,000.

"Wadannan 'yan wasan suna nuna hazaka kuma yawancinsu ba su samu damar zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ba saboda gwamnati da kamfanoni ba su kula da su ba," kamar yadda Ishiguzo ya shaida wa BBC.

"Ina jin takaici, ba sa samun tallafi ta kowane bangare."

"Suna amfani da kudinsu ne don yin wasa kuma a lokaci guda suna daukar dawainiyar kansu da iyalansu."

"Zuwa gasar babban abu ne a gare su saboda hakan zai ba su damar nuna irin bajintarsu a idon duniya kamar yadda nake yi yanzu."

Suna kokarin tara kudin ne don biyan kudin jirgi da abinci da sauran dawainiya a lokacin gasar da za a fara ranar 24 ga watan Oktoba.

Dan wasa Ishiguzo yana buga wa kungiyar nakasassu ta Arsenal a Gasar EAFA.

Kyaftin din 'yan wasan Special Eagles Emmanuel Ibeawuchi, ya nakasa sanadiyyar hadarin da ya yi lokacin da yake da shekara 22 kuma yana da burin samun daukaka kamar Ishiguzo bayan ya halarci gasar.

"Ba za mu yi watsi da burinmu ba. Mun san cewa wasanni suna karfafa gwiwar masu lalurar nakasa," in ji Ibeawuchi.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment