Monday, 1 October 2018

Yanda bikin Ranar 'yanci ya gudana a Eagle Square, Abuja

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya duba sojoji da kuma shaida faretinsu dana 'yan sanda wanda suka yi da karnukansu, a ciki hadda matasa masu bautar kasa na NYSC suma sun yi wannan fareti a Eagle Square dake babban birnin tarayya, Abuja, cikin shagalin cikar Najeriya shekaru 58 da samun 'yancin kai.Sojin sama ma sun yi shawagi da jirage a sama wanda ya kayatar da mutane sosai.
Haka kuma shugaba Buhari ya sakawa rigistar baki hannu a gurin taron.

Cikin wadanda suka halarci wannan biki na cikar Najeriya shekaru 58 da samun 'yancin kai akwai tsaffin shuwagabanni irinn su Yakubu Gowon da Abdulsalam Abubakar sai kuma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnati, Boss Mustafa da kuma shuwagabannin Kwastam da na Immigration dana sojojin dadai sauransu.


Saidai wani lamari da aka ta tattaunawa shine rashin ganin shuwagabannin majalisar tarayya, Bukolsa Saraki da Yakubu Dogara a gurin wannan taro.

A yayin da  matasa 'yan bautar kasa suka zo yin fareti, tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya mike tsaye cikin farin ciki inda ya jinjina musu.


No comments:

Post a Comment