Wednesday, 31 October 2018

Za'a sakawa kyautar gasar Laliga sunan Messi

Hukumar gasar Laliga na duba yiyuwar saka wa da ya daga cikin kyautukan da take karrama 'yan kwallo da su a karshen kakar wasa sunan Messi.


Shugaban gasar ta Laliga, Javier Tebas ne ya bayyana wa kafar watsa labarai ta Omnisport haka a wata tattaunawa da yayi dasu.

Yace, abune me kyau kirkiro wata kyauta da za'a rika karrama 'yan wasa da ita me sunan Messi, duk da cewa Javier Tebas sanannen magoyin bayan Real Madrid ne amma yace, Messi ne dan wasan da yafi dadewa a gasar dan tun yana dan karami yake bugata kuma yana kwallo da zuciya.

Kuma shine dan wasan da mafi iya kwallo da ya taba buga gasar ta Laliga dan haka zasu fitar da kyauta me sunanshi.

No comments:

Post a Comment