Saturday, 6 October 2018

Zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na PDP: Saraki ya baiwa wakilai cin hancin dala 1000

Ana can jihar Rivers shirye-shirye sun fara kankama dan zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, wakilai 4000 daga jihohin Najeriya ne zasu yi zaben wanda zai wa PDP takara.


Rahotannin da ke fitowa daga jaridar Premium Times na cewa, yanzu haka wakilan na PDP sun fara samun kudi daga gurin daya daga cikin 'yan takarar dan su zabeshi.

Kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ne ya baiwa wakilan cin hancin dala 1000 kowannensu kimanin sama da naira dubu 300 kenan.

Wasu daga cikin wadanda aka baiwa kudinne suka tabbatarwa da jaridar Premium Times hakan.

Me magana da yawun Sarakin be bayar da amsar komai ba da aka tuntubeshi akan wannan lamari, saidai wasu ma'aikatan Sarakin wanda sune suka yi aikin raba kudin sun tabbatar da wannan lamari.

Wani daga cikin wakilan yace, wannan somin tabi ne, nan gaba kudin da 'yan takarar zasu bayar zai iya kaiwa dala 4000.

No comments:

Post a Comment