Saturday, 6 October 2018

Zainab Indomie ta yi murnar samun mabiya dubu 50 a Instagram

Jarumar fina-finan Hausa da ta kwashe lokaci me tsawo ba'a ji duriyarta ba sannan daga baya ta dawo ta bayyana cewa zata ci gaba da harkar fim, Zainab Indomie ta yi murnar samun mabiya dubu 50 a shafinta na Instagram.


Haka kuma a shafukan Facebook jarumar na da mabiya dubu 83.

Sai kuma shafin Twitter inda take da mabiya dubu 13.

A sakon da ta fitar ta godewa masoyan nata da irin wannan soyayya da suka nuna mata.

No comments:

Post a Comment