Saturday, 13 October 2018

Zan so ace matan masana'antar fim din Hausa su fara fallasa mazan da su ka yi lalata da su>>Rahama Sadau

A kwanakinnan jaruman fina-finan Kasar Amurka mata sun fito da wani mataki da suka wa lakabi da Metoo wanda suke fallasa masu shirya fina-finai da kuma wasu manyan jarumai maza da suka yi lalata da su ba da son ransu ba dan su saka su a fim.


Abin bawai kan jaruman fim kadai ya tsaya ba hadda mawaka da wasu kadan daga cikin al'ummar gari.

Wannan abu ya tsallaka masana'antar fina-finan Indiya inda can ma wasu jarumai mata suka fara fallasa mazan da suka yi lalata da su ba da son ransu ba.

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi fatan cewa zata so ace suma a masana'antar fina-finan Hausa su kwaikwayi irin wancan tsari.

Rahama ta jinjina maganar, watau inda da za'a yi hakan ' Tabdijam!!!'

Wani daga cikin mabiyanta yace, wasu kam yana ganin sharri ake musu a irin wannan abu.

Saidai Rahamar ta bashi amsar cewa, duk wanda aka yiwa sharri ai yana da bakin karyatawa, kuma irin wannan abu yana faruwa a duk wata masana'antar shirya fim ta Duniya.

No comments:

Post a Comment