Saturday, 27 October 2018

Zan tashi garin Gwanin Gora idan basu daina abinda suke ba>>Gwamna El-Rufai

Biyo bayan rikicin da ya faru a garin kaduna, gidan rediyo Najeriya na Kaduna ya gayyaci gwamnan jihar a cikin shirin hannu da yawa da yake gudanarwa duk ranar Asabar wanda akayi da gwamna Rl-Rufai a yau.


An tabo maganganu da dama da suka shafi harkar gwamnati da kuma tsaro lura da yanayin da garin yake ciki.

An tambayi gwamna akan unguwannan ta Gwanin Gora dake kan hanyar zuwa Abuja wadda duk lokacin da akace ana rikici matafiya na daridari da wucewa ta unguwan.

Gwamnan ya fadi cewa ya dawo daga tafiya ya iske motoci da yawa akan hanya duk an yi cirko-cirko sun kasa shiga garin Kaduna, ya tambaya aka ce mishi ai matasa a Gwanin Gora ne suka tare hanya.

Gwamnan ya shiga gaba yace masu motocin su biyoshi.

Ai kuwa yana zuwa ya iske wasu matasa sun tare titi da tayoyi.

Gwamna El-Rufai yace, suna ganinshi suka ruga da gudu suka shiga cikin unguwa, yace amma jami'an tsaro sun bisu sun kamosu.

Gwamnan ya kara da cewa, yana kira ga manyan unguwan da cewa matasansu su dai na wannan abu, idan kuma sun ki ji, to zai tashi unguwan gaba dayanta, dan bata fi karfin gwamnati ba.

Akan maganar biyan malaman makaranta da aka sallama hakkokinsu kuwa gwamnan yace yaji wasu daga cikinsu nata sallah duk sati suna mai tofin Allah tsine to tsiwarsu can zata fada wani guri.

Yace biyan malaman makaranta ba a hannunsu yake ba yana karkashin gwamnatin kananan hukumomine amma da suka ji cewa akwai cikin wadanda aka dauka aiki sabbi da ba'a biyasu hakkokinsu ba har na tsawon watanni biyar sun mayar da aikin hannun hukumar kula da ilimi ta jiha.

Kuma akwai kudin kananan hukumomi a hanninsu, kamin su mika musu zasu tabbatar da cewa sun cire hakkokin malamannan dan a biyasu

No comments:

Post a Comment