Sunday, 21 October 2018

Zan tsaya takarar 2019>>Shehu Sani

Bayan ficewarshi daga jam'iyyar APC a jiya, Asabar, Sanata Shehu Sani me wakiltar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa nan da kwanaki kadan zai bayyana jam'iyyar da ya koma kuma zai tsaya takara a zaben 2019.


Shehu Sani ya bayyana hakane a sakon da ya fitar ta shafinshi na Facebook,

Ga abinda yace kamar haka:

Sako zuwa ga Alumman Kaduna ta tsakiya da Jihar Kaduna baki daya;A yau 20/102018 na fiche daga cikin Jamiyar APC.Nan Bada dadewa ba,zan Sanar daku Jamiyar Da zan koma da magoya baya na.Kuma zamu yi kira da kuma kuyi haka. Ina kara tabbatar maku da cewa zan tsaya takara kuma zaa hadu a final kaman inda nayi alkawari Insha Allah.Da ikon Allah zamu kubutad da talakawan Kaduna daga Halin Da suka Sami kansu a ciki Insha Allah.

No comments:

Post a Comment