Friday, 5 October 2018

Zargin Fyade: Juventus ta tafka babbar asara sadaniyyar Ronaldo: E. A Sports ta goge hotonshi daga shafinta

Tauraron dan kwallon kafa na Juventus na kara shiga cakwakiya akan maganar zargin fyade da wata mata 'yar kasar Amurka ta mai, bayan da ya ce zai rika bibiyar lamarin zargin dan wasan sau da kafa, daya daga cikim kamfanonin da yake wa talla, EA Sport ya cire hoton shi daga shafin su na yanar gizo.


Wannan dai ba karamin koma baya bane ga Ronaldon.

Juventus dai tace wannan lamari ba zai sa ta sake irin kallon da takewa Ronaldo a matsayin gwarzon dan wasa ba.

A jiya juma'a dai rahotanni sun bayyana cewa sanadiyyar wannan zargi da akewa Ronaldo Juventus din ta tafka asara inda darajar hannun jarinta ya fadi da kashi 5 cikin dari.

Juve din dai basu ce komai akan wannan lamari ba zuwa yanzu.

No comments:

Post a Comment