Monday, 1 October 2018

Zargin fyade: Ronaldo zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai, bai fito motsa jiki ba yau

A kwanannan sunan tauraron dan kwallon kafar Juventus, Ronaldo ya shiga kanun labarai saboda zargin da wata mata 'yar kasar Amurka me suna, Kathryn Mayorga ta mai na cewa ya taba mata fyade a shekarar 2009.


Ronaldo dai ya karyata wannan zargi a wani bidiyo da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta inda yace, karya take mai ta yadda suka yi abinda sukayi ba fyade ya mata ba.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Ronaldon bai fito yin atisaye da abokan aikinshi na Juventus ba a yau, Litinin, inda ake zargin ko rashin fitowar tashi na da alaka da wancan zargi na yin fyade da aka mishi.

Saidai babu cikakken bayanin me ya hana Ronaldon fitowa atisaye a hukumance. Watakila saboda bazai buga wasan da zasu buga da Young Boys bane gobe ko kuma dai wani dalilin.

The Sun tace ta ga takardun da ake zargin Ronaldon da yin fyade kuma hukuncin da ake tunanin zai iya hawa kanshi shine na daurin rai da rai.

Kathryn Mayorga dai tace Ronaldo ya bata makudan kudi dan kada ta kwarmatawa Duniya wannan labari sannan kuma ya biya wasu masu aikin kare kimar mutum su rika bibiyarta dan gano sirrin rayuwarta dan a bata mata suna.

No comments:

Post a Comment