Monday, 5 November 2018

'A kowane lokaci Obasanjo zai iya canja ra'ayi akan goyon bayan da yake wa Atiku'

Kungiyar dattawan Arewa, ACF a takaice ta bayyana shakkunta akan goyon bayan da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar akan tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.


Sakataren ACF, Anthony Sani ya bayyanawa jaridar Independent cewa Obasanjo mutun ne wanda be da magana daya kuma idan aka duba tarihin rayuwarshi za'a iya ganin haka, ya bayar da misalin cewa, Obasanjo ya yaga katinshi na jam'iyyar PDP inda yace ya daina siyasar bangaranci, daga baya ya kafa wata kungiya wadda yace ba ruwanta da siyasa wadda yace ta ceto Najeriya ce daga halin da take ciki amma daga baya ta rikide ta zama jam'iyyar siyasa.

Haka kuma Obasanjon ne dai ya ce idan ya goyi bayan Atiku akan koma menene Allah ma bazai yafe mishi ba amma sai gashi daga baya yazo yace ya yafewa Atikun kuma yana gotyon bayanshi.

Sani yace ko da shi kanshi Atikun bai da tabbacin cewa Obasanjon bazai canja ra'ayi ba kamin zabe dan shi mutum ne da bai da magana daya.

No comments:

Post a Comment