Saturday, 3 November 2018

'Abinda zan gayawa Buhari indan zan samu damar haduwa dashi'

Rahama Abdulmajid marubuciya ce, mai nazari a kan adabin Hausa, kuma mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Najeriya, musamman wadanda suka shafi mata.


A shafinta na intanet, ta wallafa wata kasida wadda a ciki ta fadi irin shawarwarin da za ta ba Shugaba Muhammadu Buhari idan da zai ba ta dama ta yi ganawar minti bakwai da shi.

Ko da yake wasu ka iya cewa akwai abubuwan da idan shugaban kasar ya aiwatar sun saba doka—misali ta ce za ta rada mashi cewa ya yi magudi, da kuma shawarar cewa ya ya kawar da kai sojoji su murkushe wata al'umma.

Shawarwarin dai sun hada da ta fuskar tsaro, "ya kara yawan jami'an tsaro a Arewa", "Ya zuba kwararru tare da ba su wani kayyadajjen lokaci na kawo karshen kasuwannin satar mutane", da kuma "Ya karbi ragamar jihar Zamfara".

Sannan ta ce za ta ba Shugaba Buhari shawara "Ya gina barikin soji a [Gonin] Gora", "ya bai wa jihohi wa'adin samar wa makiyaya wuraren kiwo", da daukar matakin ba-sani-ba-sabo a kan "fulani masu tsokana."

"Ya kafa kwamitin sarakunan gargajiya don shiga tsakani a duba matsalolin Shi'a da kokensu", da kayyade yawan muzaharorin da za su yi, "kada [su] wuce biyu a shekara", da kafa dokar hana kasha titi ga "masallatan juma'a da coci-coci da ma tarukan wa'azin kasa, maulidi, night vigils", sannan a sake Zakzaky.

"A biya shi hakkokinsa a daina amfani da kisa wajen dakile shi, a biya diyyar mutanensa".
Duk wadannan shawarwari, a cewarta, za ta ba da su ga shugaban kasar ne a minti na biyu zuwa na uku a cikin minti bakwai da ya ba ta.

Shawararwarin da za ta ba shi a bangaren tattalin arziki kuwa, a cewar Malama Rahama, su ne, "... a yi amfani da dokoki masu tsauri na hana mutumin da bai kai shekara 30 a duniya da kuma sana'a mai karfi mallakar yara sama da 3 ba".

Ko da yake ba ta yi bayani a kan takaimaimai rawar da Shugaba Buhari zai taka da wadda 'yan majalisar dokoki (wadanda alhakinsu ne yin dokoi ga kasa) za su taka wajen samar da dokar ba.

Malamar ta ci gaba da cewa za ta da shawara "a zuba malamai da kungiyoyi masu zaman kansu aikin wayar da kan al'umma tare da samar da magunguna da dabaru na tabbatar da hakan".

Bayan nan kuma ta ce za ta ba shugaban kasa shawara "A samar da kakkarfan ilmi kyauta ga duk yara hudu na kowane dan Najeriya zuwa matakin jami'a kuma kada a kara kudin jami'ar."

Sannan "maimakon sadakar da ake bai wa matasan N-Power a yi amfani da kudin wajen tilasta kirkira da koyon sana'a a bai wa kowace jiha wa'adin samar da matasa dubu dari kaza gwargwadon bukatar jihar.

"A rage kudin tallafi ga kananan manoma a zuba kudin a kan inganta noman zamani da sarrafa albarkatun noman a cikin gida".

Ta kuma ce za ta bukaci "Baba ya jogaranci wata doka ta kwanaki dari [biyu] don daidaita farashin kayan masarufi a kasar nan...don rage radadin rayuwa ga talaka.

Sannan ya tarkato wadanda ta kira "barayin gefensa" ya "hada da na PDP ya tatsa"; sai dai ba ta yi bayani a kan me take nufi da hakan ba.

Amma dai ta kara da cewa, "Sannan ya rage farashin mai ya bude ... [iyakoki] wa arewa tun da ko da aka kulle mu shekara uku mun kasa ciyar da kanmu".

Rahama ta ce daga haka, ba za ta nemi bukata ko daya ta kashin kanta ba ko da kuwa ta yin hoto da Shugaba Buhari ce.
BBChausa.No comments:

Post a Comment