Saturday, 10 November 2018

A'isha Buhari ta sake karrama jaruman Kannywood ciki hadda Ali Nuhu

A karo na biyu, uwargidan shugaban kasa, Hajiya, A'isha Buhari ta sake karrama jaruman fina-finan Hausa, wannan karin hadda Ali Nuhu, a jiya Juma'a ne jaruman da wasu masu ruwa da tsaki na masana'antar Kannywood suka je fadar shugaban kasa inda suka gana da A'isha Buhari.


Tace a ci gaba da haduwa da kwararrun masu nishadantarwa da take ta karrama jaruman masana'antar Kannywood.

A cikin wadanda aka karrama akwai, Bello Muhammad Bello, General BMB, Nazir Ahmad, Sarkin Waka, Ibrahim MaiShinku, Abdulamart Maiikwashewa, Falalu A. Dorayi dadai sauransu, muna tayasu murna.

No comments:

Post a Comment