Thursday, 8 November 2018

Ali Nuhu ya nuna alamar goyon bayan Buhari

Kusan za'a iya cewa tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu ne babban jarumi da ya rage a masana'antar fina-finan Hausa  da be bayyana wace jam'iyyar siyasa yake ba ko kuma wane dan takara yake goyon bayaba a zaben shekarar 2019 me zuwa, to saidai Alin ya nuna alamun goyon bayan Buhari.

Alin ya saka wani hoton Sadik Sani Sadik da yake sanye da rigar kamfe din shugaba Buhari.

Wannan yasa har wani ya bayyana ra'ayinshi na cewa, masana'ntar Kannywood ta koma dandalin siyasa, hakan ba abune me kyau ba.

Ali Nuhu ya mayar mishi da martamin cewa babu wani rashin kyautawa anan, kowane dan Najeriya nada 'yancin zabar abinda yake so. Su ba 'yan Najeriya bane?


No comments:

Post a Comment