Saturday, 17 November 2018

Amfani Da Illar Naira 30,000 A Matsayin Ma fi Qarancin Albashi

Naira 30,000 da gwamnatin tarayya ke jinjina biyan ma’aikatan qasar nan a matsayin sabon ma fi qarancin albashi yana iya kasancewa ya yi yawa ko kuma ya yi kaxan dangane da tattalin arzikin qasar nan.

Gwamnonin Jihohin nan dai bayan sun fito daga taron da suka yi a ranar Laraba, sun yi qorafi a kan biyan hakan, inda suka koka da cewa, in har za su biya hakan, to tabbas sai dai in za su rage yawan ma’aikatan Jihohin na su.

Sai dai, wasu qwararru sun faxi na su fahimtar a kan hakan.

Manajan Kamfanin, ‘Trispeed Consulting, Mista Rislanudeen Muhammad,’ a wata tattaunawan shi da wakilinmu a kan hakan cewa ya yi, “A gaskiya abin da ake biya a halin yanzun a matsayin mafi qarancin albashi ya yi kaxan in an kwatanta da halin da tattalin arzikinmu yake ciki.

Mista Muhammad ya ce, “Ci gaba da biyan xan abin da ake biya a halin yanzun a matsayin ma fi qarancin albashi, tamkar bayar da alawus ne kawai amma ba da sunan albashi ba.”

Ya kuma ce, sabon qarancin albashin da ake magana a kai yanzun, ba lallai ne in an biya shi a rage yawan ma’aikatan ba.

Ya yi nuni da cewa, Kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu a yanzun haka ma wasun su suna biyan sama da hakan, don haka in har gwamnati ta kasa biyan wannan xin, ma’aikata za su iya tafiya yajin aiki, wanda hakan kuma ba qaramin illa ne zai yi wa tattalin arzikin namu ba.

Wasu kuma masu sharhin cewa suke yi, za a iya biyan 30,000 a matsayin mafi qarancin albashin, amma ko an biya nan da nan zai tafi, saboda ‘yan kasuwa, masu gidajen haya da makamantan hakan su ma duk qara farashi ne za su yi.

Zai iya sanya tashin farashin kayayyaki – Farfesa Ukpong

Wani Farfesa a kan sha’anin kuxi a Jami’ar Uyo, Leo Ukpong, cewa ya yi, za a sami tashin gwaron zabin farashin kayayyaki matuqar gwamnatin tarayya ta amince da biyan Naira 30.000 a matsayin mafi qarancin albashi a qasar nan.

Da yake magana da wakilinmu, Farfesa Ukpong cewa ya yi, ai da zaran an bayar da sanarwar qarin albashin, farashin kayayyaki za su tashi.

Ya ce, kamata ya yi gwamanti ta cije a kan biyan hakan a matsayin mafi qarancin albashin, a maimakon hakan kamata ya yi ta yi amfani da kuxin wajen qara gina wasu masana’antun da za su samar da ababen bukata na yau da kullum, wanda zai sanya farashin kayyakin ya sauka a Kasuwa.

Ya ce, ai da zaran an shelanta amincewa da sabon mafi qarancin albashin, qananan ‘yan Kasuwa masu motocin sufuri, masu qananan kamfanoni duk za su qara farashin kayayyakin su.

A maimakon hakan, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta qirqiro wasu sabbin shirye-shirye da za su tilasta faxuwar farashin kayayyaki aqalla da kashi 15 a Kasuwanni, hakan ya fi da ta qara albashin da kashi 50 cikin 100, in ji qwararren.

Sai dai cibiyar Kasuwanci ta Abuja, (ACCI) ta nuna goyon bayanta ga yin qarin sabon mafi qarancin albashin da Naira 30,000.

Kamfanoni masu zaman kansu sun yi nasu martanin

A kan matsayin kamfanoni masu zaman kansu na Abuja, babban daraktan Kamfanin ACCI, Tonia Shoyele, cewata yi, tuni ya kamata a ce an samar da sabon mafi qarancin albashin, in an yi la’akari da yanda farashin komai ya tashi.

Da take magana a kan ko kamfanoni masu zaman kansu za su iya biyan mafi qarancin albashin in har an amince da shi, Shoyele tace, a yanzun haka abin da muke biya a Kamfaninmu ya fi sabon mafi qarancin albashin da ake magana a kai, wanda hakan ke nuna lallai kamfanonin za su iya biya.

Ta qara da cewa, sabon mafi qarancin albashin zai wa Kamfanoni masu zaman kansu amfani, domin da zaran gwamnati ta biya kuxin kamfanonin ne kuxin za su komo.

Ta yi kira ga dukkanin sassan biyu da su yi qoqarin cimma wata matsaya na mafi qarancin albashin wanda zai baiwa ma’aikatan daman yin rayuwa mai kyau duk da tashin farashin kayayyakin.
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment