Monday, 5 November 2018

An Ba Buhari Wa'adin Kwanaki 14 Ya Binciki Ganduje

Kungiyar fafitikar kare 'yancin dan Adam ta SERAP ta baiwa Shugaba Muhammad Buhari wa'adin kwanaki 14 kan ya gaggauta binciken Gwamnan Kano, Umar Ganduje bisa zargin karbar rashawa daga hannun 'yan kwangila.

Kungiyar ta yi barazanar garzayawa kotu don tilasta gwamnatin tarayya kan ta gudanar da bincike kan wannan zargi da ake yi wa Gwamnan. A halin yanzu dai, majalisar dokokin jihar Kano ta yi nisa wajen gudanar da bincike kan wannan zargin.
Rariya.

No comments:

Post a Comment