Wednesday, 7 November 2018

An bawa direban da ya kashe 'yan bindiga 2 a Zamfara kyautar miliyoyi

Wani direban motar haya, da ba a bayyana sunansa ba, ya karbi tukuicin Naira miliyan 2 daga gwamnatin jihar Zamfara a matsayin ladan kisan wasu 'yan bindiga 2 a satin da ya gabata.


Da yake bashi kyautar kudin amadadin gwamnatin jihar Zamfara, kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Bello Dankande, ya ce kyautar kudin cikon alkawarin da gwamnatin jihar ta yi ne na bawa duk wanda ya kwace bindiga 1 daya daga hannun 'yan ta'adda tukuicin Naira miliyan N1m.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar direban ya yi arangama da 'yan bindigar ne a kan hanyar zuwa Gidan Jaja/Gurbin Bore a daren jiya.

Direban ya kashe 'yan bindigar ne yayin da su ke kokarin tsallaka titi rataye da bindigoginsu a wuya.
Legit.ng

No comments:

Post a Comment