Tuesday, 27 November 2018

An dakatar da sarakunan Zamfara daga aiki kan barayin shanu

Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta ce ta dakatar da wasu sarakuna daga mukamansu bisa zarginsu da alaka da 'yan fashin shanu da masu garkuwa da mutane.


Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar, Alhaji Bello Dankande, ya shaida wa BBC cewa an dakatar da hakimai uku sannan na hudu ya gudu.
"Duk wani basaraken da ka ga mun dakatar, mun samu labari yana mu'amala da wadannan 'yan ta'adda. Misali, akwai wani uban kasa da aka kawo mana korafi a kansa cewa, na daya, ya tura galadimansa ya karbi belin barayi daga hannun 'yan sanda.
"Haka kuma ya karbi kudi daga hannun wani dan ta'adda. Mutanen garin sun zo sun ce ya karbi N50,000," in ji kwamishinan.
Ya kara da cewa za a gudanar da bincike kan hakiman sannan a tube rawuyan da ke kansu "kafin a gabatar da su a gaban shari'a."
Matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma ta barayin shanu ta yi kamari a jihar Zamfara, inda a wasu lokutan barayin suke kashe mutanen da suka sace.
Ko da a makon jiya sai da wasu rahotanni suka ce an bayar da kudin fansa kafin a sako wasu tagwaye 'yan mata da aka sace a jihar.
Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment