Saturday, 10 November 2018

An fara horas da 'yansandan Dubai amfani da babur me tashi sama

Hukumar 'yansandan birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa sun fara horas da jami'ansu akan amfani da wani babur me tashi sama da zasu rika aiki dashi a cikin birnin.


Wani kamfanin kasar Amurkane ya kera baburan kuma ya shaida cewa ko guda nawa Dubai din take bukata zasu samar mishi dasu, kamfanin ya bayyana cewa ko da mutum guda, ba sai hukuma ba ko kamfani ba, zai iya sayen babur din, saidai kamin a sayarwa da mutum sai an tabbatar da ya iya amfani dashi kamar yanda CNN ta ruwaito.

Babban daraktan 'yansandan Dubai, Brigadier Khalid Nasser Alrazooqi ya bayyana cewa zasu yi amfani da babur dinne dan kaiwa ga guraren dake da wahalar shiga ta kasa kuma wannan babur me tashi zai fara aiki a Dubai nan da shekarar 2020.

No comments:

Post a Comment