Monday, 26 November 2018

An fara sayar da bidiyon Gwamna Ganduje na karbar daloli a kasuwannin Kano

A jihar Kano an fara sayar da bidiyon dake nuna gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudin cin hanci kamar yanda jaridar Daily Nigerian ta zarga, ana sayar da faifan bidiyon ne a kasuwanni da guraren tsayuwar ababen hawa.Wannan hoton wani ne da ya sayi faifan bidiyon wanda aka sawa sun Gandolors yake nunawa a shafinshi na sada zumunta.

Gwamna Ganduje dai ya nemi kotu da ta dakatar da jaridar ta Daily Nigerian daga ci gaba da wallafa bidiyon nashi wanda ya zuwa yanzu sun kai 6, haka kuma ya bukaci jaridar da ta biyashi diyyar biliyan 3 saboda bata mai suna.

No comments:

Post a Comment