Saturday, 24 November 2018

An gano wata sabuwar halittar da ba'a sani ba me shekaru miliyan 200

Wata halitta da aka gano me girman gaske wandda aka yi kiyasin girman ta yakai na giwa ta baiwa masana kimiyya mamaki matuka.


Halittar wadda bincike ya nuna cewa ta rayu wajan shekaru miliyan dari 200 da suka gabata an gano kasusuwantane a kasar Poland, kamar yanda shafin Express Uk ya ruwaito, sannan abinda ya fi bayar da mamaki akan halittar shine masana kimiyya sun yi amannar cewa be kamata a samu irin wannan halitta a shekaru miliyan dari 200 da suka gabata ba domin halittu masu girma irin nata sun rayune a shekaru miliyan 250 da suka gabata.

Saboda ba'a taba ganin wannan halitta ba yanzu dai masana kimiyya sun saka mata sunan Lisowicia Bojani.


No comments:

Post a Comment