Wednesday, 7 November 2018

An kammala ginin katafariyar gadar 'Yan Kura dake Kano: Kalli kayatattun hotuna

Wannan doguwar gadarnance ta 'yan Kura wadda ta hada da Bata da Triumph a birnin Kano, rahotannin dake fitowa daga jihar Kanon na cewa zuwa yanzu an kammala ginin Gadar sauran kaddamarwa.


Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gaji aikin gadar daga gwamnatin Kwankwaso a lokacin da aikin yake a mataki na kashi 25 cikin 100, kamar yanda me baiwa gwamnan Kano din shawara ta fannin kafafen sadarwa, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana.

Nan da watan Disamba ne ake sa ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai je Kanon dan kaddamar da wannan aiki.

No comments:

Post a Comment