Thursday, 1 November 2018

An Sake Samun Motsin Kasa A Abuja Yau

Hukumar da ke kula da albarkatun karkashin kasa ta Nijeriya ta bada sanarwar sake samun motsin kasa a yankin Maitama na Abuja, da misalin karfe 12:26 na ranar yau Alhamis.


Wannan shine karo na biyu da aka samu motsin kasa a Abujan, a kwanakin bayan an samu motsin kasan a wani yanki na Mpape da kuma Maitaman, zuwa yanzu hukumar ba ta bada wani cikakken karin bayani akan mostin kasar ba.
Leadershiphausa.

No comments:

Post a Comment