Tuesday, 27 November 2018

An shawo kan gobarar daji da ta yi ajalin mutane 85 a Amurka

An shawo kan gobarar daji da ta yi ajalin mutane 85 a Amurka
Ya zuwa mutae 85 ne suka mutu a gobarar daji da aka samu nasarar shawo kanta a jihar California ta Amurka wadda ta kama tun ranar 8 ga watan Nuwamba.


Labaran da jaridun Amurka suka fitar na cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne aka gama kashe gobarar dajin da aka ba wa suna "Gobarar Sansani".

Sakamakon sake gano jikkunan wasu mutane 2 ya kawo adadin wadanda gobarar ta kashe zuwa mutane 85.

A lokacinda ake ci gaba da neman wasu mutane 251 da suka bata a gobarar, hakan ya sa ake fargabar adadin wadanda suka mutu na iya daduwa.

Gobarar ta kama a yankin Paradise na arewacin jihar California a ranar 8 ga Nuwamba inda ta cinye gidaje kusan dubu 14 da wuraren aiki kusan 514, da ma wasu karin gine-gine dubu 4,265.

Gobarar ta mamaye waje mai girman kilomita 620 inda ta isa ga wani bangaren na jihar Chicago.

Gobarar sansani ita ce gobara mafi muni da ta afku a jihar California ta Amurka.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment