Saturday, 17 November 2018

An wanke gwamna Ganduje daga wata Cakwakiya da aka so sake sakashi

Munji labarin motocin bas dinan kirar Hyundai H1 kimanin 100 da aka ce an gansu a jihar Legas na yakin neman zaben shugaba Buhari, bayan bayyanar motocin an rika rade-radin cewa wai gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Gandujene ya siyawa Buhari su.


Motocin dai na dauke da suna  GOBIR kuma ainahin wanda ya saye su ya bayyana inda ya karyata ikirarin farko.

Yakubu Gobir sunan wanda ya sayi motocin, dan kasuwane kuma dan siyasa.

Ya fito ta dandalinshi na sada zumunta ya bayyana cewa, shine ya bayar da motocin ga Buhari da Osinbajo da kuma jam'iyyar APC dan ayi kamfe amma ba Gwamna Ganduje ba.

Yace shi za'a kai kara ba Ganduje ba. Kuma idan akwai me tambaya akan wannan lamari yana iya yi mai.

Wani ya tambayeshi cewa me zai hana yayi amfani da kudin sayen motocin wajan taimakawa talakawa tunda dai ko da su ko basu in Allah ya yarda Buhari zai sake cin zabe?

Gobir ya bashi amsar cewa, dama can yana da motocin a ajiye, yayi amfani dasu ne lokacin da yake neman a tsayar dashi taka wanda bai yi nasara ba. Yace dan hakane yanzu ya baiwa shugaba Buhari dan yayi Kamfe.

No comments:

Post a Comment